MATAR UBA Chapter 23 By Milhart

MATAR UBA Chapter 23 By Milhart: “What’s wrong with me? What’s wrong me? You’re here kissing this thing and you’re here asking me what am I doing? tell me what you’re doing with him?”

Cikin rashin fahimta Tace ” What? Are you kidding me? Am I kidding you” magana yake ransa a mugun ‘bace idanunsa sun canza daga Farare zuwa jaa, ran Badiyya yayi matukar ‘baci Rai a d’an ‘bace Tace “Hashim Anya kana cikin hankalin ka kuwa?”

“Ke zan tambaya Badiyya, but is okay…. Is okay” Yana maganar Yana dariya had’e da kuka Yana d’aga kafad’a Yana Kai Nan yayi ficewar sa,duk gun kallon sa a ka tsaya yi, abokin Ammar ne ya d’auki mic yace “Please we are sorry,DJ ka samana kid’a” Nan suka cigaba da shashewar su, Badiyya Kan Ammar ta nufa ganin ya fasa baki sannan gefen idon sa ya kumbura hakan ne yasa suka je clinic aka wanke Masa ciwin, banda sorry babu abinda take cewa masa ji take kamar taje ta Rama Masa a fad’in ta baida hujjan dukkan sa.

Hashim kai tsaye d’akin sa ya wuce zama yayi akan one sitter daje d’akin sa, d’an kwanciya yayi Yana kallon saman d’akin hawayene masu zafi suke sauko masa,da zarar ya rufe idanunsa Badiyya yake gani da Ammar, tsaki yayi yace “kin cuce Ni Badiyya,ki rasa Wanda Zaki kula sai Ammar har kiss?” A bayyane yake maganar.

“Hashim Kennan, kana matsala wallahi kishin ka yayi yawa yanzu Dan Allah me amfanin abinda kayi?”

‘dago idanunsa yayi don kallon Wanda yake magana d’an tsaki yayi ya ce “Look Farees baka ga abinda na gani ba ne Dole kace haka”

“Hakane ni banga abinda ka gani ba….” Zama yayi a bakin gado Jana ya d’aura da fad’in “Babu yanda za a yi idanuna su gane min abinda ka gani,sabida kaga Ni da hankali na”

Gyara Zama yayi yace “Okay idan na fahimce ka Farees kana nufin mahaukacine Ni bani da hankali ki”

‘yar karamar dariya yayi yace ” Kai kace hakan Ni bance maka mahaukaci ba,Amma me ma difference d’in ka da mahaukacin? Ka tsaya kana ta ihu akan rashin gaskiya,kace min kana da hankali?”

“Farees na roke ka Dan Allah ka kyale Ni naji da abinda yake damina”

Rai a ‘bace ya mike yace “anki a kyale ka Kai Kennan ba hali a fad’a maka gaskiya? Na Sha fad’a maka ba haka ake soyayya ba,Amma baka ji,nifa da idona Naga sanda da buge shi da hannun ta Bata sani ba, shiyasa take hura Masa ido”

A tsawace yace “Kar ka Raina min hankali Mana inga tana kissing d’insa kace min ba Haka ba”

“You see your life kaga shine illan tab’a jikin ta da kake yi,kana kissing d’inta ba Dole kayi zargin ta ba, me bakayi da ita, shaidar da zan maka d’ayane shine nasan bazaka yi Zina da ita ba but nasan babu abinda baka sani ba a jikin ta ba,Kuna ganin hakan waye wane” tsaki Mai tsawo ya jaaa ya fice, sai Kuma ya leko yace “Faisal ya Kiran yace Yana Kiran ka baya shiga idan ka gama haukan naka sai ka Kira shi” ya ja kofar ya rufe Masa yayi tafiyar sa.

Farees cousin brother d’in Faisal ne, hakan yasa Hashim Faisal da Farees suka zama abokai.

Tsaki Hashim yayi ya koma ya zauna Hashim kasa bacci yayi tunda ya zauna Bai tashi ba sai tsaka wa yake da warwara Yana kallon kofar d’akin a ganin sa Badiyya zata Zo ta Bashi hakuri kamar yadda ta Saba,Amma Bata Zo ba,Bai tashi a gun ba sai da lokacin sallah tayi bayan ya idar da sallah yace “Baza ta Zo ta bani hakuri ba Kenan Hmm,ko da yake ma hakurin me zata bani tunda tana son hakan?”

Badiyya ma hakan take ba tayi bacci ba sai kallon wayar ta take ko zai kirata ya Bata hakuri Amma shiru kake a fili Tace “Wato bazai Kiran ba Kenan bayan yasan yayi laifi a tunanin sa zan je na Bashi hakuri ko? To wannan karon Kan karyan ka Tasha Karya” ta cigaba da harkar gaban ta.

Projects d’insu suke kokarin had’awa hakan yasa makarantar busy, Yau kwanaki uku Kenan Badiyya Bata Zo inda yake ba Haka ma Hashim bai nema ta.

Department d’in su Badiyya ya shiga, Badiyya na ganin sa tayi Murmushi a zuciyar ta Tace “Nasan zaka dawo” ga mamakin ta sai taga ya wuce ta Baki a bud’e ta bishi da kallo, Hashim Sarai ya ganta Amma yayi kamar bai ganta ba, inda ya hango Farees ya nufa dake course d’in badiyya da Farees d’aya.

Farees na ganin sa ya ‘bata Rai, hannu Hashim ya Mika Masa had’e da fad’in “Assalamu Alaikum”

Farees Mika Masa hannu yayi ya amsa chan ciki ba don ya so ba.

Zama Hashim yayi yace “Ina ka shiga ne haka two days ba a ganin ka?”

Farees yace ” Ni d’in kuwa?….. Ina Nan ba a dai neman ba” sai ganin Hashim yayi Farees ya Fara tattara takardun sa, cikin rashin fahimta Hashim yace “A’a Ina kuma zaka?”

“Bacci nake ji zanje na kwanta”

“Bacci Kuma to Muje man” ya tashi da niyar bin sa Farees yayi saurin fad’in “No thanks bakaji bacci nace ma zanyi ba?” Yana Kai Nan Bai tsaya Jin me Hashim zai ce ba ya bar gun. Hashim jikin sa sanyi yayi murmushin takaici yayi yace “To Allah ya kyauta.”

Badiyya na kallon su duk da bata Jin su ta gane akwai matsala, hakan yasa tayi ficewar ta, Hashim Zama yayi Yana kallo a wayar sa duk ji yake baya Jin Dadi,ba Masoyiyar sa Babu abokin sa,tsaki yayi sa wayar a jaka,ya fice.

AFTER THREE DAYS

Badiyya ganin Hashim yaki kulata hakan yasa ta shiga tashin hankali, sukan samu misunderstanding Amma Basu wice kwanaki biyu sun shirya idan yayi yawa 3 days, hakan yasa ta shiga Kiran sa,Yana gani har cikin ransa yaji dad’i har ya sa hannu da niyar d’aga wayar sai ya tuno abinda ya gani sai yayi saurin d’auke hannun sa, Yana ji ya na gani ta jera Masa missed calls biyar.

Badiyya cikin murya kuka Tace “Ammar he refused to pick my calls”

“No Don’t say that maybe he is sleeping or something else please think always think postive”

” You won’t understand Ammar I know Hashim very well he is not sleeping,and whenever he saw me he keeps on ignoring me repeatedly”

“Don’t think about it too much Badiyya, nasan Hashim Yana sonki kawaii dai yayi fushi Ne kuma kema ai kin san halin sa,tunda shi d’in ba bakon ki bane”

Murmushin takaici Badiyya tayi Tace ” Balqees Kenan ko da yake kin fad’i gaskiya Amma sanin Kanki ne bai tab’a fushi har haka ba,abin ma mamaki yake bani”

(Balqees kawar Badiyya yace, Ruwa biyuce Mahaifin ta ba indiye ne mahaifiyar ta Kuma bafulana ce,fulanin Gombe (bajoga) duk da zaman su yafi yawan India hakan bai hanata iya hausa da fulani sosai ba).

“Hakane Kam Bai tab’a hakan ba,Amma kema ai da laifin ki tunda kin San halinsa Kuma kina sonsa bai kamata ki bari har Ku Kai three days baku shirya ba”

Gyaran murya Ammar yayi yace “, Alright you people won’t stop speaking hausa right”

A tare sukace “sorry ”

Yace ” it’s alright but please Badiyya, if he didn’t call you go and meet him”

Ta amsa da ” Okay”

Yace “No no, Promise me you’ll meet him”

“I promise I’ll meet him”

Nan suka cigaba da hirar su.

Karfe 10 saura na dare zaman jiran Kiran sa take Amma shiru,hakan yasa ta d’auki gyallen ta ta yafa, minti goma ya d’auke ta Isa kofar gidan wani dogon ajiyar zuciya tayi kana,ta kwankwasa kofar had’e da kusa kanta cikin d’akin, Hashim karar bud’e kofar yaji hakan yasa ya bud’e sleepy eyes d’insa ya d’aura idon sa a kanta,kau da Kai yayi kana yace “what brings you here?”

Murmushin takaici tayi Tace ” Magana nake so muyi”

” Dawa? ”

” Dakai Mana”

A hankali yace “idan ina bukatar hakan ko? ”

“At least Hashim ka tashi Mana muyi Magana dan Allah, tun fa da na shigo kake kallon bango, ko kallo na bakayi ba”

“Bana bukatar ganin ki Diyya”

” Hashim me yasa kake da taurin Kaine Dan Allah? Yanzu kana nufin ka rabu dani Kenan?”

” Eh” kawai yace a takaice,

Zagayowa tayi ta zauna a bakin gadon tana kallon sa, hawayen da ta gani a idon sa ne yasa ta Fara kuka, Tace “Hashim Dan Allah Kar ka Mana haka, ya kamata kayi bincike Kan ka yanke hukunci a kaina”

Tashi yayi tsaye sa hannun said yayi a aljihun three quarter wandon sa ya juya Mata baya, Kana yace “wani bincike ya rage nayi? Bayan Ni Nan ganaune ba jiyau ba” Yana maganar Yana d’an bubbuga faffad’ar kirjinsa

Cikin shesshekar kuka Tace “Wallahi tallahi ba abinda kake tunani bane kawai…..” Juyo wa yayi a tsawace “kawai me? Nace kawaii me Diyya? Baki da abinda Zaki fad’a min, dama na dad’e ina zargin ki dashi Kuma kin tabbatar min da zargina”

Fashe wa tayi da kuka Mai sauti Tace ” am sorry please Hashim kana tsorata ni ban tab’a gannin ka acikin irin wannan halin ba,kayi hakuri ka yarda dani Dan Allah”

” In yadda dake Kika ce? Hmm” ya share hawayen dake fuskar sa kana ta d’aura da fad’in “Ta ina kike so Na yarda dake,idan da dagaske kike ai da tun a ranar zaki nemi muyi sulhu Amma Baki Zo ba,sai d’azu Zaki kirani,sai da muka d’auki two weeks”

” Nasan Kana fushi ne shiyasa na bari ka huce”

A tsawace yace ” To hell with you Diyya,I hate you”

Tashi tayi Tace “Karya kake Hashim you love me Hashim and you’ll forever do”

Murmushin gefen baki yayi ya d’aura hannayen sa a kunkunmin sa yace “Okay haka kikace?”

“Eh Haka nace,Kuma haka yake”

“Alright,get out of my room”

Yana Maganar Yana nuna Mata kofa

Cike da mamaki ta nuna kirjin ta Tace “Ni? I should get out?”

“Yes get out”

“Hashim Ni kake cewa na fita a d’akin ka?”

“Eh ke waye ce ke da ba zan ce ki fita ba? Kawai malama ki fice min daga d’aki”

Huci tayi Tace “Okay naji zan fita,Amma Hashim tell me one thing ya kake so muyi da su Daddy da mummy? Kasan cewa dawowar mu kawai ake tunda an Mana baiko”

“Wannan Kuma ke ta shafa ki fad’a wa iyayen ki cewar Ni Hashim Ahmad Shettima na janye Maganar auren dake tsakani na da ke”

Badiyya ganin Hashim dagaske yake tace “Kar kamin haka hashim,zaka sai Mana dariya”

” Tunda ke baza ki fita ba Ni bara na fita bar Miki d’akin”

Wayar say ya d’auka ya nufi hanyar fita sai da yazo daf kofar yace “Idan kin gama ki rufe min kofar” yayi ficewar da, Badiyya bin bayan sa tayi da kallo ita gani take abin kamar Wasa Amma dagaske yake,zama tayi a bakin gado ta shiga kuka sai da tayi Mai isarta kana ta shiga toilet ta wanko fuskar ta, tana fitowa da fice daga d’akin ta rufe Masa kofar kamar yadda yace ta ajiye Masa makulli a inda yake ajiyewa.

Yana ganin fitowar ta yayi saurin d’aura waya a kunnen sa kamar Yana waya, kallon sa ta tsayi tafi minti biyar tana kallonsa,Hashim ganin zata iya Karya Mata zuciya hakan yasa yayi saurin barin gun, kad’a Kai tayi ta fice da ga compound d’in.

Yana ganin ta tafi ya koma d’akin,kwanciya yayi Yana jallony saman d’akin yana tunanin happy moments da sukayi spending da ita,tabbas Yana kaunar ta Amma bazai iya auranta ba.

Badiyya bata gaji da bibiyarsa ba,amma ganin wulakancin a yake Mata hakan yasa ta hakura,har suka kammala projects d’insu Bai bari sun hadu ba haka Kuma baya picking calls d’inta d’ga bisa ni yayi blocking d’in ta,ya goge duk wani abun da ya shade ta, number ne kad’ai ya bari Shima Kuma bai San dalilin da yasa ya kasa gogewa ba.

NIGERIA

A tsawace yace “Baka da hankali dama ban sani ba? Ni kake so ka kunyata a idon duniya Hashim?”

Kai a kasa yace “No daddy ba haka bane, babu yanda za’a yi na jawo maka abin kunya,Amma idan ka bari aka d’aura aure na da Badiyya shine abun kunya ba auren ta ba”

Zama Daddy yayi yace ” Me yasa kace haka,akwai wani abinda ya kamata na sani wanda ban sani ba?”

“Eh Daddy”

” Uhmn ina sauraron ka” Maida hankalin sa yayi don ya fahimci inda Maganar tasa ta dosa, bai rage komai ba haka Bai Kara komai ba, Mummy dake zaune tun d’azu akan sofa Tace “Kai Hashim kaji tsoron Allah ka fad’a mana gaskiya dukkanin mu mu mun San Badiyya yarinya ce mai tarbiya”

” Hakane Mummy amma Badiyya da kuka sani a baya dabance da ta yanzu”

Ta amsa da ” Allah ya kyauta”

Suka amsa da “Ameen”

Daddy yace “Tashi ka je zan duba na ga yanda za’a yi”

Yace “Toh Daddy na gode”

Ya tashi ya fice.

Daddy Maida kallon sa yayi ga Mummy yace “Amina,ya kike ganin zamu b’ullowa al’amarin yaran nan,wallahi kaina ya kulle”

” Nima haka Alhaji,to Amma ya zamuyi yaron Nan dai shi ga yarinyar Nan yace Yana so,Kuma yanzu yace ya fasa bai kamata mu sa shi yin abinda baya so ba”

“Okay idan ma fahimce ki,so kike na janye Maganar auren sa da Badiyya Kar ki manta fa, Mahaifin yarinyar Nan amini na ne fa,idan na Masa haka ai ban kyauta Masa ba”

” Hakane Alhaji,Amma ya kamata ka Sani yaran yanzu ka haife sune Amma baka haifi halinsu ba,tunda yace baya so a janye Maganar Kar Kuma a Zo Ana da na sani”

“Kai Amma banji Dadi ba ko kad’an yanzu ban San yanda zan tin Kari Alhaji Usman ba”

” Ka kwantar da hankali Alhaji,yanzu tunda dama jiran su Hashim ake a had’a auren su day Fadeelah ina ga kawai gara a Sanar dasu ayi bikin Nan Nan da wata d’aya”

“Toh Shikenan zan duba na gani”

Tashi yayi yace “bari na watsa ruwa idan yaso zan nemi shi Mahaifin Suraj d’in in yaso zanje har gida na Sami Usman muyi Magana ta fahimta don wannan ba Maganar waya bace”

“To alhaji a fito lafiya,kamun Nan bara na kawo maka abinci”

“A a hajiya bar abincin Nan duk ina ji ba Ni da appetite”

“Toh Shikenan yanda kake so hakan za’ayi.”

Bayan ya fito Kai tsaye ya zarce gidan su Badiyya, ya Sanar da mahifin ta Akan cewar Hashim ya janye Maganar auren yarsa, sannnan ya bashi hakuri, Alhaji Usman mutum ne Mai hakuri sannan ya d’auki hakan a matsayin kaddarar Badiyya, ya Kuma Masa alkawarin hakan bazai shafi abotar su ba,yayi Masa godiya ya tashi ya koma gida,ya sanar da mummy yanda sukayi jikinta yayi sanyi matuka.

Tace “banji dadin abin Nan ba Sam,Nima insha Allah gobe da safe zanji Ni gidan nasu na bawa mahaifiyar ta hakuri, yanzun ma don dare yayi ne da naje”

” Sai Kuma kiyi,duk laifin kine duk kin bi kin sangarta yaro”

Yana kai Nan ya haura sama sai surutai yake ya na d’aga hannu.

Mummy Tace “Oh ‘ya ‘yan kuka mai jawo wa uwar sa jifa,Allah shi kyauta” sai ji tayi yace “Ameen” ba tayi tunanin yaji ba hakan yasa tayi ficewa daga part d’in say ta koma part d’inta, hashim ta tarar a parlor a kishingide kana ganin sa kasan Yana cikin damuwa,cewa tayi “Damuwa ko? Baka ga komai ba tukanna”

“Haba mummy ya kuma Zaki ce haka?”

“Me kake so Na ce maka Hashim? Tunda burinka shine kaci mutuncin Mahaifin ka,to yaje gidan su Badiyya an janye auren hankalin ka ya kwanta?”

Ji yayi kirjin sa na duka uku uku, wani hawaye ne masu zafi suka Fara zubowa daga idanunsa yace “an janye?”

Ta amsa da “Eh hankalin ka ya kwanta ko? Mu Kuma ka tada Mana namu”

Jin shesshekar kukan sa yasa tayi saurin kallon sa Tace “Hashim!!! Kuka?”

Baice Mata komai ba, tayi saurin karasowa inda yake ta dafa shi a kafad’a Tace “Hashim ya kuma Naga kana kuka ba Kai kace baka son auren ba?”

Ya d’aga Mata Kai alamun eh, Tace “To Kai da ya kamata kayi farin ciki Mai yasa kake kuka?”

“mummy ina fa sonta”

” And so? Kuma kace baka sonta, Wai me yake faruwane?”

Kwantar da kansa yayi a kafad’ar ta, yayin da ita Kuma take d’an bubbuga Masa baya, a dai dai Nan Daddy ya shigo yace “Ga irinta Nan ai kina Nan kina lalata yaro”

“Amma Alhaji baka ga halin da yake ciki bane?”

” To sai me ya mutu Mana, mtsww Dan Allah ki d’auko min chaja na ki kawo min d’aki yanzun Nan”

Ya yi ficewar sa

Daddy yayi fushi sosai, don dakyar yake amsa Masa gaisuwa Amma hakan Bai Hana Hashim basa hakuri ba, daga bisani ya huce.

An d’aura auren Fadeelah da Suraj cikin farin ciki da kaunar juna.

BAYAN SHEKARA ‘DAYA

mummy na zaune a parlor tana kallon News kwasam taga Ana sanarwa jirgi yayi hatsari from Dubai to Nigeria, aciki harda wannan shahararren Dan kasuwa Mai suna Alhj Ahmad Shettima, mummy hannu ta sa a Kai ta saki Kara a gun ta yanke jiki ta fad’i.

Hashim da already yaji Labarin mutuwar Mahaifin Nasa yayi saurin dawowa gida daga gidan su faisal, shigowar sa Kenan yaji news din da take ji, Kan ya nufi ta harta yanke jiki ta fad’i.

KARANTA: MATAR UBA Chapter 24 By Milhart

Leave a Comment