MATAR UBA Page 13 Hausa Novel

Advertisements

MATAR UBA Page 13 Story Written By Milhart: Asiyah in tambaye ki Mana?” “Ina sauraron ki” “Ranar da Kika kwana a gidan mu bata tambaye ki a ina Kika Kauna ba? ” Murmushin tayi kana Tace “ke ma kin San jazaman ne wannan, har Saida ta kusa dukana ma”

“Ya salam, Dan Allah Asiyah ki dawo gidan mu, ki rabu da mutanen Nan, so suke su kashe ki misali ranar da ta Koro ki yanzu da sun cutar dake Kuma fa, daba don taimakon Allah da taimakon mutumin Nan ba da yanzu Labari ya Sha ban ban”

” Laa kin tuna min ma mun sake had’u wa dashi” Gyara Zama shamsiyya tayi Tace ” Haba Dan Allah da gaske kike?”
“Eh wallahi da gaske nake mun gaisa na mishi godiya, har ya fad’a min sunan sa”

“Mene ne sunan nashi?”

Advertisements

” Hashim”
” Wow hashimu”
” Shamsiyya nifa Hashim nace Miki”
” Toh Hajiya ai ainahin sunan Kenan”
” Toh iyani naji, Kinga na daukoy uniform na islamiya yau ba sai na koma gida ba”
” Yauwa yafi ai, sai biya ta gidan mu Kan Muje islmiyar ko? ”
” Tih Shikenan ba matsala.”

Nan suka cigaba da hirar su har Mai driver din shamsiyya yazo,Kai tsaye gidan su shamsiyya suka nufa, bayan sunci abinci sunyi sallar la’asar ya Kai su Islamiyya.

Baraka tunda ta samu tayi wanka taji saukin azabar da take ji, tana fita ta kwanta Bata d’au lokaci Mai tsawo ba baccin wahala yayi awon gaba da ita.

Yesmin tunda ta dawo daga school ta Shiga d’akin taga mummyn ta na bacci ta jaa Tsaki had’i da fad’in “Mata Bata da aikin yi sai bacci” tana Kai Nan ta Maida kofar ta rufe, kitchen ta nufa ta girki Abinda zata sa cikin ta, bayan ta gama ne ta ta Shiga ta watsa ruwa kana ta yi Sallah ta fito garden ta zauna a Kan kujera tana chat tana sipping five alive, horn da taji a gate ne yasa ta Maida kallon ta a gun, Mai gadi da sauri ya leka ta karamar gate don ganin wane ne.

A nitse yake tafiya cikin nitsuwa ya gaida shi “Ina wuni baba”
Ya amsa da “lafiya Lau ‘dan Nan”
“Baba Dan Allah tambaya nake”
“Toh Allah yasa na sani”
“Asiyah nake nema”

Baba Mai gadi mamaki ne ya Kama shi, a zuciyar sa yace “Asiyah ake nema a Karo na farko ban tab’a ganin an Zo neman ta ba Allah yasa dai lafiya”
A fili Kuma yace “Lafiya kake neman ta?”
” Dama…… ”
Muryar shamsiyya ne ya katse shi tana fad’in “Mai gadi Wai wane ne haka?”
Tana maganar ta karasa ta fito waje, tsuman tsaye tayi don ganin kyawun sa, Hashim ganin kallon yayi yawa ce “Sannun ki” ta amsa da “yauwa San sannu, how may I help you?”
“Dan Allah Asiyah nake nema”
Wani Abu Taji ya tokare ta a kirji da kyar ta samu ta sai saita kanta Tace “Asiyah da fatan dai Lafiya?”
“Eh lafiya Lau,jiya ne ta manta tray d’inta a bakin hanya shine na kawo Mata.”

Wani irin kallo ta Masa ta ce “Dama Kuna had’uwa ne?”
“Eh to, ban San yanda zance Miki ba dai, kawatace”
” Kawa?”
” Eh please don’t think otherwise, na lura Bata gida ko?”
” Eh Bata Nan”
” Islamiya taje ne?”
” Ni dai ban sani ba”
” Ba Yar uwar ki bace”
” Yar Uwa Tace”
” Kuma kice Baki San inda taje ba” tab’e baki yayi had’e a d’aga kafad’a Wanda hakan ya zame Masa jiki, sai ya d’aura da fad’in “Any ways ganan tray d’in da ta manta” Yana Mika Mata ya juya da niyar tafiya, da sauri Tace “To in ta dawo wa za’a ce Mata?”
Murmushi yayi Wanda ya nuna kyawun fuskar sa ya nuna dimple d’insa, d’an juyawa yayi yace “kice Mata Hashim Ahmad Shettima.”

Zaro Ido tayi tace “Hashim Ahmad Shettima?”
Bai tanka manta ba ya shige motar sa ya bar gun, ganin tsayuwar da take bazai amfane ta da komai ba, ta shige Ciki, Zama tayi a garden d’in Taji zaman ba dad’i ta jaa tsaki ta shige d’akin ta.

Kwanciya tayi akan gado tayi ruff da Ciki, a bayyane Tace “Hashim Ahmad Shettima, tabbas ina Jin Labarin guy d’in Amma ban tab’a tunanin kyawunsa ya Kai haka ba”

*WANE NE HASHIM AHMAD SHETTIMA?*
Hashim Ahmad Shettima d’ane ga Alhaji Ahmad Shettima, Ahmad Shettima shahararren d’an kasuwa ne Wanda yayi suna idan baizo a na farko ba, zai zo a na biyu, hakan yasa Bai fiye Zama ba yawanci a kasar waje yake business d’in sa, matar sa d’aya Hajiya Amina da ‘ya ‘ya biyu Hashim da Fadeelah,a sanadiyar neman na halal d’insa jirgin su ya fad’i ya Kone kurmus, iyalan sa sun Shiga tashin hankali sosai Amma babu yanda suka iya kullu nafsin za’ikatul maut.

Bayan rasuwar Alhaji Ahmad, Suraj Wanda ya kasance PA d’in Alhaji Ahmad ya Auri Fadeelah suna zaune cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali Babu abinda ta rasa har ta Haifa masa Yara biyu Adnan da islam, Hashim Kuma bayan rasuwar mahaifin nasu ya Koma kasar waje karatu ya karanci business, bayan ya gama ya dawo gida ya Fara kula da harkokin Mahaifin nasa.
Wannan shine cikekken tarihin Hashim.

“Hashim ‘din Soyayya yake da Asiyah? Kai it can’t be” tashi tayi tana kaiwa tana kawo wa ” Dole na San abin da zanyi akai, sabida na kamu da son sa bugu da Kari Yana da kud’i Dole na rarrashi Mummy ta nema min mafita.”

A Haka bacci ya d’auke, Hashim na tuki mamaki yake a zuciyar sa yace “Wannan wani irin gidane haka, tabbas yarinyar da na gani Yar uwartace don suna mugun Kama, Amma daga shigar ta kasan Yar hutu ce , Amma Asiyah kayan jikin ta duk a kod’e? Hatta uniform d’in da na Fara ganinta dashi a yage suke, Kai Dole na fad’ad’a bin cike akan ta, I need to help her.”

Zaro wayar sa yayi a aljihun rigar sa ya yi dialing number faisal, Faisal daga d’ayan ‘bangaren ya amsa da “Yane mutumina?”
“Kalau fa kana ina?”
“Ina gidan su zee”
” Mtswws Kai kullum sai ka jene, baka gajiya? ”
” Gajiya haba malam ai gaya maka idan kaga na daina zuwa to nayi wuff da ita ne”
” Hmm to Allah ya kyauta yanzu ya za’a yi? Ina son ganin ka, ko na zone?”
” A’a malam idan na gama zan Zo har gida na same ka Kar ka rage min hanzari”
“mtsww zakaji dashi ai, sai kazo”
Sai ya katse wayar, ya Koma gida Yana zaman jiran zuwan sa.

Maman Yesmin tunda ta Koma gida ihu da nishin Boko da Baraka ne ya tsaya Mata a rai duk hankalin ta ya tashi wani irin feelings take ji, da zaran ta tuna sai ta taune baki Nan take marar ta ya Fara ciwo, sai saki take ta jaa a fili tace “Kai wallahi auran soja ma matsala ne yanzu ina bukatar mijina ba hali”

Wayarta ta d’auko ta bud’e Facebook account da sunan Maman Yesmin, Nan da Nan akayi ta turo Mata friend request, Kun San maza da zaran sun ga sabon account anyi ta rushing ana turawa request, tun da Fara accepting request a kwance take a gun har akayi sallar Maghriba da Isha bata tashi a gun ba, dake Yesmin ta tafi hutu, ita kad’ai ce a gidan.

Ana cikin hakan tayi arba da wani request Mai suna *Zahra Yar less* , da sauri ta bud’e profile d’in ta duba Tace “Wow garin mu d’aya” profile picture ta bud’e ganin hoton wasu Mata tsirara suna alfasha ta sake taune bakin ta, ganin nayi ta cire zanin jikin ta, ware kafafun ta tayi a kishingid’e ta Fara satisfying kanta, Ni ko da na hakan nayi sauri na fita na jaa Mata kofar nayi gaba abina.

*HASHIM*
“To gani duk kabi ka Dame Ni da Kira Wai ya akayine kam?”

“Faisal please Ina so Kan taimake ni ne”
“Ina sauraron ka taimako wani iri Kenan?”
” Maganar yarinyar Nan Asiyah”
Kallon sa Faisal yayi yace “Asiyah Kuma wace ce ita d’in?”
“Asiyah ta Mana,Wacce muka ganta ranar a GRA? ”
” Oh kace min yarinyar da ka kusa kashe mu a kanta”
” Koma dai mene ne, tunda ka gane ta buri na ta cika, ina son yarinyar Nan so na aure? ”

Gyara Zama Faisal yayi yace “Aure ka tabbata auren ta kake son yi kuwa?”
“Eh na tabbata so nake na aure ta, na gama Rayuwata da ita sabida ina sonta sosai”
“To yanzu me mafita kaga bamu San gidan su ba ko?”
“na sani”
“lallai dagaske kake har ka Nemo gidan su?”
” Tsaya Nan ai Wanda yake son d’an tsuntsu shi ke binsa da jifa”
” Ba shakka hakane yanzu idan ka shirye sai muje”
“alright Amma ba yanzu ba ina so na fahimci wani Abu a tattare da ita tukunna”
” Me Kennan Hashim? ”
” Zan Sanar da Kai when the time comes”
” Kan ka akeji in tayi tsami zumuji”
Murmushi kawaii Hashim yayi, sukayi ta Hira har sai da akayi sallar Maghrib Faisal ya Koma gida.

*BAYAN KWANA BIYU*
Hashim ya Shiga damuwa tashin hankali na rashin ganin ta, ko Wacce Rana sai ya fita ya yi parking a layin su Asiyah Amma baya ganin ta sai ya dawo gida Rai a ‘bace ya daina kula kowa sai dai ya shige d’akin sa ya kulle kofa.

Da Sallama ta Shiga katafaren parlor bin parlon take da kallo ganin yanda ya had’u har sai da ta Raina gidan su ta shagala sosai wajen kallon makeken hoton Hashim dake manne a bangon d’akin, motsin da taji a bayan tane ya dawo da ita daga tunanin da ta Lula, Murmushi tayi kana Tace “Sannu da zuwa yarinya”
“Yauwa Sannu ina wuni hajiya”
” Lafiya kalau zauna Mana”
Tana muna Mata sofa dake gefen ta, Zama tayi kana Wacce ta Kira da hajiya Tace “Gashi Kuma kamar ban gane ki ba”
Tana maganar tana sake Mata kallo ko zata gane ta.

Gyara Zama tayi Tace “Baki sanni ba,asali ma yau ne Kika Fara gani na a Rayuwar ki”
” Oh to to madallah, ya zan taimaka Miki?”
“Hajiya suna na Safiya, Hashim nazo nema”
Kallon ta ta sake yi dakyau, kana Tace ” Hashim kike nema?”
Ta amsa da “eh” da fatan dai Lafiya ko?”
” Eh lafiya lau”
” Aiko hashim baya Nan ya fita”
Dafe Kai tayi kamar wata Mai Jin ciwon kai, kana Tace ” Kash to Shikenan” ta mike ta d’aura da fad’in ” Ni zan tafi sai anjima”
” To mu Jima dayawa”
Tasa Kai ta fice, tab’e baki hajiya tayi Tace ” Oh yaran zamani ba kunya har gida,har gida kizo neman na Miji? To Allah kashirya Mana” ta shige ta.

Fitar safiya ke da wuya ta hango motar Hashim, Murmushi tayi had’e da Dariya karasawa tayi inda yayi parking, tabbas yayi mamakin ganin ta cikin sauri ya fito yace “Lafiya me Kika Zo yi anan?”
“Nazo wurin Kane so nake muyi wata magana
“Okay, Zo Muje mu zauna a chan”
Yana nuna Mata garden dake d’an nesa dasu, ba b’ata lokaci suka Isa gun suka zauna, babu wanda ya furta komai Hashim ganin shirun yayi yawa ya gyara murya yace “Ya dai since zamuyi magana Kuma kinyi shiru?”
Murmushi tayi kana Tace “Hashim na San baka sanni ba, baka ma San suna na ba”
Yace “hakane”
“Suna na Safiyya kanwace a gun Asiyah”
“Umm ina sauraron ki”
” Hashim tun raanar da na Fara Jin sunan ka naji kana burge Ni,bani da buri illa na ganin ka, sai Kuma gashi Allah ya kawo Kan gidan mu a saukake,tun ranar da na Fara ganin ka hankalina ya kasa kwanciya naji na kamu da son ka, I love you hashim”
Murmushi yayi yace ” Dan Allah da gaske kike ko wasa?”
Murmushi tayi kana Tace “dagaske nake am in love with you.”

“hakan ba matsala bane don kin Soni, Amma Ni Asiyah nake so,am in love with her, zamu iya Zama abokai in ba matsala”
Shiru tayi sannan tace “To Shikenan naji” ta mike da niyar tafiya, hashim Shima mikewa yayi yace “tafiya Zaki yi? Ki tsaya ko ruwan sanyine a kawo Miki”
“A a nagode” ta juya tayi tafiyar ta, tana ji Yana Kiran sunan ta tayi burus dashi, tab’e Baki yayi ya d’aga kafad’ar sa ya d’aura da fad’in “chan Miki” ya shige cikin gida.

Comment & Share

KARANTA:

MATAR UBA Page 9 Hausa Novel

DANGIN UBANA Page 14 By Milhart

Advertisements

Leave a Comment